Al-Kahf 18:48
الكهفوَعُرِضُوا۟ عَلَىٰ رَبِّكَ صَفًّا لَّقَدْ جِئْتُمُونَا كَمَا خَلَقْنَـٰكُمْ أَوَّلَ مَرَّةٍۭ ۚ بَلْ زَعَمْتُمْ أَلَّن نَّجْعَلَ لَكُم مَّوْعِدًا
Kuma a gittã[1] su ga Ubangijinka sunã sahu guda, (Mu ce musu), "Lalle ne haƙĩƙa kun zo Mana, kamar yadda Muka halitta ku a farkon lõkaci. Ã'a, kun riya cẽwa bã zã Mu sanya mukuwani lõkacin haɗuwa ba."
[1] Bayãnin abũbuwan da ke aukuwa a wurin hisãbi ke nan ga mãsu bin son zũciya, su bar sharĩ'a.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net