Al-Kahf 18:46
الكهفٱلْمَالُ وَٱلْبَنُونَ زِينَةُ ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا ۖ وَٱلْبَـٰقِيَـٰتُ ٱلصَّـٰلِحَـٰتُ خَيْرٌ عِندَ رَبِّكَ ثَوَابًا وَخَيْرٌ أَمَلًا
Dũkiya da ɗiya,[1] sũ ne ƙawar rãyuwar dũniya, kuma ayyuka mãsu wanzuwa na ƙwarai sun fi zama alhẽri a wurin Ubangijinka ga lãda kuma sun fi alhẽri ga bũri.
[1] Dũkiya da ɗiya, ƙawar dũniya ne, idan suka zama abin alfahari ga mai su, amma idan an ciyar da dũkiya ga tafarkin Allah, kuma aka karantar da ɗiya ga bisa tafarkin hanyar sharĩ'a suka tãshi Musulmin ƙwarai, to, sun zama aikin sharĩ'a na Lãhira kħ nan.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net