Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 18 · Aya ta 42

Al-Kahf 18:42

الكهف

وَأُحِيطَ بِثَمَرِهِۦ فَأَصْبَحَ يُقَلِّبُ كَفَّيْهِ عَلَىٰ مَآ أَنفَقَ فِيهَا وَهِىَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ عُرُوشِهَا وَيَقُولُ يَـٰلَيْتَنِى لَمْ أُشْرِكْ بِرَبِّىٓ أَحَدًا

Ma’ana

Kuma aka halaka dukan 'ya'yan itãcensa, sai ya wãyi gari yanã jũyar da tãfunansa biyu, sabõda abin da ya kashe a cikinta, alhãli kuwa ita tanã kwance a kan rassanta, kuma yanã cẽwa, "Kaitõna, dã dai ban tãra[1] wani da Ubangijina ba!"

[1] Ya yi nadãmar halakar gõnar kawai, amma bai yi nadãmar kãfircin shirkin da ya yi ba, sabõda haka Allah bai mayar masa da badalinta ba. Daga nan kuma anã fahimtar cewa rashin mai da al'amari ga Allah shirku ne, kuma girman kai sabõda dũkiya, shirku ne wanda ƙawar dũniya ke sanya wãwãye a ciki.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Kahf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net