Al-Kahf 18:4
الكهفوَيُنذِرَ ٱلَّذِينَ قَالُوا۟ ٱتَّخَذَ ٱللَّهُ وَلَدًا
Kuma Ya yi gargaɗi ga waɗanda[1] suka ce: "Allah yanã da ɗa."
[1] Lãrabawa sun ce malã'iku 'ya'yan Allah ne. Yahũdawa sunce Uzairu ɗan Allah ne, Nasãra sun ce Ĩsã ɗan Allah ne. Bãbu ladabi ga faɗin wannan magana. Sabõda haka Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya gaya musu, cewa wannan magana ƙarya ce kuma rashin ladabi ne ga Allah, da ba su yi ĩmãni ba, ya ji tsõro kada ya zama shĩ ne ya yi ƙwauron bãki ga faɗã musu gaskiya. Sai Allah Ya gaya masa, cewa kada ya halakar da ransa dõmin baƙin cikin haka.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net