Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 18 · Aya ta 102

Al-Kahf 18:102

الكهف

أَفَحَسِبَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓا۟ أَن يَتَّخِذُوا۟ عِبَادِى مِن دُونِىٓ أَوْلِيَآءَ ۚ إِنَّآ أَعْتَدْنَا جَهَنَّمَ لِلْكَـٰفِرِينَ نُزُلًا

Ma’ana

Shin fa, waɗanda suka kãfirta sun yi zaton (daidai ne) su riƙi waɗansu bãyĩNa[1], majiɓinta baic iNa? Lalle ne, Mun yi tattalin Jahannama ta zama liyãfa ga kãfirai.

[1] Waɗanda suka riƙi wasu bãyin Allah, sunã bauta musu, kamar Yahũdu mãsu bauta wa Uzairu da Nasãra mãsu bautawa Ĩsã da wasu Musulmi mãsu bauta wa wasu sãlihai sun zama kãfirai. Ma'anar bautawar shi ne su ƙirƙira wasu hukunce-hakunce kõ wasu sifõfi waɗanda suka sãɓa wa maganar Alƙur'ãni da Hadĩsi, sa'an nan su jingina su zuwa ga waɗannan bãyin Allah, su bi su da su.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Kahf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net