Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 17 · Aya ta 79

Al-Israa 17:79

الإسراء

وَمِنَ ٱلَّيْلِ فَتَهَجَّدْ بِهِۦ نَافِلَةً لَّكَ عَسَىٰٓ أَن يَبْعَثَكَ رَبُّكَ مَقَامًا مَّحْمُودًا

Ma’ana

Kuma da dare, sai ka yi hĩra[1] da shi (Alƙur'ãni) akan ƙãri gare ka. Akwai tsammãnin Ubangijin ka Ya tãyar da kai a wani matsayi gõdadde.

[1] Hĩra da Alƙur'ãni, watau a yi sallõlin nãfila na dare, shafa'i bibbiyu, a ƙãre da wutri. Ga Annabi tahajjudi da wutrin wãjibi ne ƙãri a kan abin da aka ɗõra wa sauran mutãne, a lõkacin da yake zaune a gida. Ga sauran mutãne wutri sunna ce, kamar sallõlin ĩdi da rõkon ruwa da husũfin rãnã da na wata. A nan akwai bambanci a tsakãnin Annabi da jama'arsa a wajen wutri.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Israa

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net