Al-Israa 17:42
الإسراءقُل لَّوْ كَانَ مَعَهُۥٓ ءَالِهَةٌ كَمَا يَقُولُونَ إِذًا لَّٱبْتَغَوْا۟ إِلَىٰ ذِى ٱلْعَرْشِ سَبِيلًا
Ka ce: "Dã akwai waɗansu abũbuwan bautãwa tãre da shi, kamar yadda suka faɗa, a lõkacin, dã (abũbuwan bautãwar) sun nẽmi wata hanya[1] zuwa ga Ma'abũcin Al'arshi."
[1] Dã su abõkan tãrayyar sun nemi hanya zuwa ga Allah dõmin su yãƙe shi sabõda Ya ce Al'arshi Tãsa ce, Shi kaɗai, dõmin su sãmi nãsu rabon, sabõda Al'arshi tã haɗiye kõme, har da su.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net