Al-Israa 17:26
الإسراءوَءَاتِ ذَا ٱلْقُرْبَىٰ حَقَّهُۥ وَٱلْمِسْكِينَ وَٱبْنَ ٱلسَّبِيلِ وَلَا تُبَذِّرْ تَبْذِيرًا
Kuma ka bai wa ma'abũcin zumunta hakkinsa[1] da miskĩna da ɗan hanya. Kuma kada ka bazzara dũkiyar ka, bazzarãwa.
[1] Hakkin zumunta shi ne alheri da sãdar da zumunta. Hakkin miskini da ɗan hanya zakka da sadakar taɗawwa'i da liyãfar kwana uku ga bãƙo bisa al'ada da alheri, bã bisa ɓarna da kallafãwa ba.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net