Al-Israa 17:110
الإسراءقُلِ ٱدْعُوا۟ ٱللَّهَ أَوِ ٱدْعُوا۟ ٱلرَّحْمَـٰنَ ۖ أَيًّا مَّا تَدْعُوا۟ فَلَهُ ٱلْأَسْمَآءُ ٱلْحُسْنَىٰ ۚ وَلَا تَجْهَرْ بِصَلَاتِكَ وَلَا تُخَافِتْ بِهَا وَٱبْتَغِ بَيْنَ ذَٰلِكَ سَبِيلًا
Ka ce: "Ku kirayi Allah[1] kõ kuwa ku kirãyi Mai rahama. Kõwane kuka kira to Yanã da sũnãye mafi kyau. Kuma, kada ka bayyana[2] ga sallarka, kuma kada ka ɓõye ta. Ka nẽmi hanya a tsakãnin wancan."
[1] Muƙarana a tsakãnin sũnayen Allah waɗanda ake kiran sa da su wajen rõƙo da waɗanda bã a yin roko da su. Sũnãyen mafiya kyau da ake kiran Allah da su Hadĩsi ya kãwo su sai a nħma daga Jalãlaini.
[2] Kuma tsakaitãwa wajen karãtun salla ko addu'a kamar yadda aikin Annabi ya nũna yadda ake yi, kada a bayyana kada a ɓõye. Sai dai tsaka.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net