Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 16 · Aya ta 91

An-Nahl 16:91

النحل

وَأَوْفُوا۟ بِعَهْدِ ٱللَّهِ إِذَا عَـٰهَدتُّمْ وَلَا تَنقُضُوا۟ ٱلْأَيْمَـٰنَ بَعْدَ تَوْكِيدِهَا وَقَدْ جَعَلْتُمُ ٱللَّهَ عَلَيْكُمْ كَفِيلًا ۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَعْلَمُ مَا تَفْعَلُونَ

Ma’ana

Kuma ku cika da alkãwarin[1] Allah idan kun yi alkawari, kuma kada ku warware rantsuwõyinku a bãyan ƙarfafa su, alhãli kuma haƙĩƙa kun sanya Allah Mai lãmuncẽwa a kanku. Kuma lalle Allah ne Yake sanin abin da kuke aikatãwa.

[1] Wanda yake rantsuwar alkawari da wani, sa'an nan ya warware rantsuwar dõmin neman ya ƙulla wata rantsuwa da wani mutum sabõda wani amfãninsa kõ jama'arsa a cikin wata kabĩla wadda ta fi ta mutãnen farko ƙarfi to, siffarsa kamar mace ce mahaukaciya, mai yin zare, a bayan ta tukka shi, ya yi ƙarfi, sa'an nan ta warware shi. Sabõda haka idan ta so mayar da shi wani zare, to, bã zai yi kyau ba kamar zaren farko da ta yi kuma mutãne sun gãne haukarta, bã zã su yi wata ma'ãmala da ita ba. Wanda ya yi rantsuwa da Allah a kan abu, to, yã sanya Allah lãmuni ke nan. Bã ya halatta ga wanda ya shugabantar da Allah ga wani abu, sa'an nan ya kõma bãya ya ƙi cika wannan alkawarin dõmin bai kiyãye girman Allah ba, wanda ya sanya a tsakaninsa da abõkin ma'ãmalarsa. Tsaron alkawari ni'ima ne.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Nahl

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net