An-Nahl 16:58
النحلوَإِذَا بُشِّرَ أَحَدُهُم بِٱلْأُنثَىٰ ظَلَّ وَجْهُهُۥ مُسْوَدًّا وَهُوَ كَظِيمٌ
Kuma idan aka yi wa ɗayansu bushãra da mace[1] sai fuskarsa ta wuni baƙa ƙirin, alhãli kuwa yanã mai cike da baƙin ciki.
[1] Fahintar cewa ɗã namiji da'ya mace duka ɗaya suke, da hana kashe su kõ turbuɗe su, wata ni'ima ce babba da 'yancin mãtã babba, a cikin rãyuwar ɗan Ãdam.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net