Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 16 · Aya ta 125

An-Nahl 16:125

النحل

ٱدْعُ إِلَىٰ سَبِيلِ رَبِّكَ بِٱلْحِكْمَةِ وَٱلْمَوْعِظَةِ ٱلْحَسَنَةِ ۖ وَجَـٰدِلْهُم بِٱلَّتِى هِىَ أَحْسَنُ ۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ ۖ وَهُوَ أَعْلَمُ بِٱلْمُهْتَدِينَ

Ma’ana

Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima[1] da wa'azi mai kyau kuma ka yi jãyayya da su da magana wadda take mafi kyau. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMafi sani ga wanda ya ɓãce daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.

[1] Kira zuwa ga hanyar Ubangiji, Allah, yanã daga cikin abũbuwan kõyo daga Ibrãhĩm kuma kira zuwa ga Allah na daga cikin ni'imõmin Allah ga mai kiran da wanda ake kiran sa'an nan zaman kiran da hikima da wa'azi mai kyau, ni'ima ce ga mai yi da waɗanda ake kira zuwa ga shiriyar duka. Abin da ake cħwa Hikima shĩ ne a yi magana a kan hujja wadda abõkin husũma bã zai iya kauce mata ba.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Nahl

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net