Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 16 · Aya ta 115

An-Nahl 16:115

النحل

إِنَّمَا حَرَّمَ عَلَيْكُمُ ٱلْمَيْتَةَ وَٱلدَّمَ وَلَحْمَ ٱلْخِنزِيرِ وَمَآ أُهِلَّ لِغَيْرِ ٱللَّهِ بِهِۦ ۖ فَمَنِ ٱضْطُرَّ غَيْرَ بَاغٍ وَلَا عَادٍ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ

Ma’ana

Abin sani kawai (Allah) Ya haramta[1] muku mussai da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah game da shi. Sa'an nan wanda aka tĩlastaa kan jama'a kuma baicin mai zãlunci, to, lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.

[1] Bayãnin abũbuwan da aka haramta, idan bãbu larũra. Anã cin abin da shari'a ta hana a ci a kan larũra sai idan larũrar ta sãmi mutum ne a cikin hãlin sãɓon Allah, kamar mai fita daga ɗã'ar sarkin Musulunci ya yi tãsa ƙungiya dabam, kõ wanda ya fita dõmin wani zãlunci kamar sãta ga misãli, to, ba su cin haram dõmin su ci gaba da aikinsu.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Nahl

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net