Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 15 · Aya ta 95

Al-Hijr 15:95

الحجر

إِنَّا كَفَيْنَـٰكَ ٱلْمُسْتَهْزِءِينَ

Ma’ana

Lalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu[1] izgili.

[1] Mãsu tsananin izgili ga Annabi waɗanda Allah Ya isar masa daga gare su su biyar ne, daga Bani Asad bn Abdul'uzza bn Kusayyi akwai Aswadu bn el Muttalib, Abu zam'ah, kuma daga Bani Zuhrah akwai el Aswad bn Abdu Yagũth. Daga Bani Makhzumi akwai el walid bn Mugira. Daga Bani Sahmi akwai el Ãs bn wã'il. Daga Banĩ Khuzã'a akwai el Harith bn el-Tulãtilah. Su ne mãsu darajar mutãnensu. A lõkacin da suka dõge da sharri, Allah Ya hũtar da Annabi daga sharrinsu da nau'i-nau'i na masĩfu suka halaka. Dubi ƙarin bayãni daga tafsĩrin bn Kathĩr. tsare Annabi daga gare su, tun yanã shi kaɗaia Makka yã isa ya sanya shi ya dõgara ga Allah bãyan abubuwa sun ƙãra yawa da sauƙi.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Hijr

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net