Al-Hijr 15:92
الحجرفَوَرَبِّكَ لَنَسْـَٔلَنَّهُمْ أَجْمَعِينَ
To, rantsuwa da Ubangijinka![1] Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya.
[1] Allah Ya yi rantsuwa da ZãtinSa a kan Shĩ ne Ubangijin Annabi Muhammadu tsira da aminci su tabbata a gare shi, dõmin Ya natsar da ransa daga tsõron mãsu yi masa izgili, kuma dõmin Ya ƙarfafa shi ga zartar da aikin da Ya sanya shi na iyar da Manzanci bã da wata fargaba ba.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net