Al-Hijr 15:29
الحجرفَإِذَا سَوَّيْتُهُۥ وَنَفَخْتُ فِيهِ مِن رُّوحِى فَقَعُوا۟ لَهُۥ سَـٰجِدِينَ
"To idan Na daidaitã shi kuma Na hũra daga RũhĩNa[1] a cikinsa, to, ku fãɗi a gare shi, kunã mãsu yin sujada."
[1] Wannan ya nũnã Ãdamu an yi halittarsa ne da lãka da Rũhi daga Allah kamar yadda aka halitta Isã, amincin Allah ya tabbata a gare shi. Sabõda haka halittar Ãdamu ta fi zama abin mãmãki daga halittar Ĩsã, dõmin Ĩsã asali guda kawai ya rasa daga halittar ɗiyan Adam ta al'ãda, amma halittar Ãdamu tã rasa dukan asalan biyu na uwa da na uba. Haka kuma halittar Hawwã'u, matar Ãdamu tã fi ta Ĩsã ban mãmãki dõmin rashin asalin uwa da ta yi inda ɗã yake ɗaukar lõkacin sũrantãwa, ya fi ban mãmãki daga rashin asalin uba.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net