Ibrahim 14:28
ابراهيمأَلَمْ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ بَدَّلُوا۟ نِعْمَتَ ٱللَّهِ كُفْرًا وَأَحَلُّوا۟ قَوْمَهُمْ دَارَ ٱلْبَوَارِ
Shin ba ka lura ba da waɗanda suka musanya[1] ni'imar Allah da kãfirci kuma suka saukar da mutãnensu a gidan halakã?
[1] Kuraishãwa wadanda Allah Ya yi musu ni'imar zama a cikin hurumin Allah da aminci da Ya zuba a kansu da albarku, sun musanya gõdiya da kãfirci a lõkacin da suka ƙaryata Manzon Allah. Sun saukar da mutãnensu a gidan halaka a Badar.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net