Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 14 · Aya ta 19

Ibrahim 14:19

ابراهيم

أَلَمْ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ خَلَقَ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ بِٱلْحَقِّ ۚ إِن يَشَأْ يُذْهِبْكُمْ وَيَأْتِ بِخَلْقٍ جَدِيدٍ

Ma’ana

Shin, ba ka gani ba cẽwa lalle ne Allah Yã halicci sammai bakwai da ƙasa da mallakarSa.[1] Idan Yã so zai tafiyar da ku, kuma Ya zo da wata halitta sãbuwa.

[1] Dalĩli ne a kan kãfircin kãfirai ba ya rage mulkin Allah da kõme, domin bã su iya fita daga halittar sammai da ƙasa, waɗanda Allah Ya halitta da abin da yake mallakarsa.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Ibrahim

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net