Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 13 · Aya ta 28

Ar-Ra'd 13:28

الرعد

ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَتَطْمَئِنُّ قُلُوبُهُم بِذِكْرِ ٱللَّهِ ۗ أَلَا بِذِكْرِ ٱللَّهِ تَطْمَئِنُّ ٱلْقُلُوبُ

Ma’ana

Waɗanda suka yi ĩmãni kuma zukãtansu sukan natsu da ambaton Allah. To, da ambaton Allah[1] zukãta suke natsuwa.

[1] Ambaton Allah, shĩ ne bin hukunce-hukuncensa ga kõme. Umar ɗan Khattãb ya ce: "Mafificin ambaton Allah, shi ne wanda aka yi a wurin umurninsa ko haninsa. Wanda yake yin zikirin bãki ba da yanã aiki da hukunce-hukuncen Allah ba a cikin ibãdarsa da mu'amalarsa, to, shi mai izgili kawai ne da sũnan Ubangijinsa, ba mai yin zikiri ba ne.".

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Ar-Ra'd

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net