Yusuf 12:88
يوسففَلَمَّا دَخَلُوا۟ عَلَيْهِ قَالُوا۟ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْعَزِيزُ مَسَّنَا وَأَهْلَنَا ٱلضُّرُّ وَجِئْنَا بِبِضَـٰعَةٍ مُّزْجَىٰةٍ فَأَوْفِ لَنَا ٱلْكَيْلَ وَتَصَدَّقْ عَلَيْنَآ ۖ إِنَّ ٱللَّهَ يَجْزِى ٱلْمُتَصَدِّقِينَ
Sa'an nan a lõkacin da suka shiga gare shi suka ce: "Yã kai Azĩzu! Cũta ta shãfe mu, mũ da iyãlinmu, kuma mun zo da wata hãja maras kuma. Sai ka cika mana ma'auni, kuma ka yi sadaka a gare mu. Lalle ne Allah Yanã sãka wa mãsu yin sadaka. "[1]
[1] Wannan ya nũna ba a haramta sadaka ba ga Annabãwan da suka gabãta, sai ga Annabinmu Mahammadu, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, shĩ da danginsa na kusa aka hana wa cin sadaka.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net