Yusuf 12:85
يوسفقَالُوا۟ تَٱللَّهِ تَفْتَؤُا۟ تَذْكُرُ يُوسُفَ حَتَّىٰ تَكُونَ حَرَضًا أَوْ تَكُونَ مِنَ ٱلْهَـٰلِكِينَ
Suka ce: "Tallahi! Bã zã ka gushe ba, kanã ambaton Yũsufu,[1] har ka kasance Mai rauni ƙwarai, kõ kuwa ka kasance daga mãsu halaka."
[1] Mai tsõhon laifi bã ya son ya ji anã ambatonsa, sabõda haka ('yan'uwan Yũsufu) suke zargin bãbansu da ambaton (tuna) Yũsufu.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net