Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 12 · Aya ta 77

Yusuf 12:77

يوسف

قَالُوٓا۟ إِن يَسْرِقْ فَقَدْ سَرَقَ أَخٌ لَّهُۥ مِن قَبْلُ ۚ فَأَسَرَّهَا يُوسُفُ فِى نَفْسِهِۦ وَلَمْ يُبْدِهَا لَهُمْ ۚ قَالَ أَنتُمْ شَرٌّ مَّكَانًا ۖ وَٱللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا تَصِفُونَ

Ma’ana

Suka ce: "Idan ya yi sãta, to, lalle ne wani ɗan'uwansa yã taɓa yin sãta a gabãninsa." Sai Yũsufu ya bõye[1] ta a cikin ransa. Kuma bai bayyana ta ba a gare su, ya ce: "Kũ ne mafi sharri ga wuri. Kuma Allah ne Mafi sani daga abin da kuke siffantãwa."

[1] 'Yan'uwan Yũsfu sun faɗi cewa ɗan'uwan Binyaminu ya taɓa yin sãta, dõminsu nũna cewa a wajen ubansu tsarkakakku ne daga yin sãta. Shi kuma wanda ya yi sãtan ya gade ta ne daga wajen uwarsa, dõmin wani shaƙĩƙinsa(Yũsufu) ya taɓa yin sãta. To, sai Yũsufu ya ce a ransa: "Kũ ne dai mafi sharrin mutãne, Allah ne Mafi sani daga abin da kuke siffintãwa." Asalin wannan magana wata goggonsa ce (Shi Yũsufu) ɗiyar Is'hãƙa, ta riƙe shi, yanã yaro, har a lõkacin da ubansa (Yãƙũbu) ya so ya karɓe shi daga gare ta, sai ta yi kaidin sanya kãyan sãta a cikin rigarsa (Yũsufu) dõmin ta hana uban ɗaukarsa. A wata ruwaya kuma an ce shi (Yũsufu) ya ɗauke wani mutum mutumi ne na zĩnãri (gunki) ya karairaya shi. Don haka 'yan'uwansa suke jingina sãta a gare shi.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Yusuf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net