Yusuf 12:56
يوسفوَكَذَٰلِكَ مَكَّنَّا لِيُوسُفَ فِى ٱلْأَرْضِ يَتَبَوَّأُ مِنْهَا حَيْثُ يَشَآءُ ۚ نُصِيبُ بِرَحْمَتِنَا مَن نَّشَآءُ ۖ وَلَا نُضِيعُ أَجْرَ ٱلْمُحْسِنِينَ
Kuma kamar wancan ne Muka bãyar da ĩko ga Yũsufu a cikin ƙasa[1] yanã sauka a inda duk yake so. Munã sãmun wanda Muke so da rahamar Mu, kuma bã Mu tõzartar da lãdar mãsu kyautatawa.
[1] Lõkacin da Yũsufu yanã aikin tattalin arzikin ƙasa a cikin shekarar wadãta, ya Mallakeƙasar Masar duka a lõkacin da wahala da yunwa suka auku.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net