Yusuf 12:51
يوسفقَالَ مَا خَطْبُكُنَّ إِذْ رَٰوَدتُّنَّ يُوسُفَ عَن نَّفْسِهِۦ ۚ قُلْنَ حَـٰشَ لِلَّهِ مَا عَلِمْنَا عَلَيْهِ مِن سُوٓءٍ ۚ قَالَتِ ٱمْرَأَتُ ٱلْعَزِيزِ ٱلْـَٔـٰنَ حَصْحَصَ ٱلْحَقُّ أَنَا۠ رَٰوَدتُّهُۥ عَن نَّفْسِهِۦ وَإِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ
Ya ce: "Mẽne ne babban al'amarinku, a lõkacin da kaka nẽmi Yũsufu daga kansa?" Suka ce: "Tsarki ga Allah yake! Ba mu san wani mummũnan aiki a kansaba." Mãtar Azĩz ta ce: "Yanzu fagaskiya[1] ta bayyana. Nĩ ce nã nẽme shi daga kansa. Kuma lalle ne shĩ, haƙĩƙa, yanã daga mãsu gaskiya.
[1] Da wannan magana ta mãtarAzĩz Zalĩha anã fahimtar ita tã musulunta ta hannun Yũsufu kãfin a ɗaure shi.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net