Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 12 · Aya ta 30

Yusuf 12:30

يوسف

وَقَالَ نِسْوَةٌ فِى ٱلْمَدِينَةِ ٱمْرَأَتُ ٱلْعَزِيزِ تُرَٰوِدُ فَتَىٰهَا عَن نَّفْسِهِۦ ۖ قَدْ شَغَفَهَا حُبًّا ۖ إِنَّا لَنَرَىٰهَا فِى ضَلَـٰلٍ مُّبِينٍ

Ma’ana

Kuma waɗansu mãtã[1] a cikin Birnin suka ce: "Matar Azĩz tanã nẽman hãdiminta daga kansa! Haƙĩƙa, yã rufe zũciyarta da so. Lalle ne mũ, Munã ganin taa cikin ɓata bayyanãnna."

[1] Tsegumin mãtã a cikin gari da yadda mãtar Azĩz ta yi maganin tsegumin, ta hanyar yiwa mãtan liyafa. Mace bã ta kunyar mãtã 'yan'uwanta ga irin wannan fitina idan ta sãme ta, ita kaɗai, balle mãtã ga sũ duka sun kãmu a cikin tarkon da ya kãma ta. Sai ta gaya musu gaskiyar abin da ya auku a tsakãninta da Yũsufu, a bãyan ta rãma zargin da suka yi mata.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Yusuf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net