Yusuf 12:20
يوسفوَشَرَوْهُ بِثَمَنٍۭ بَخْسٍ دَرَٰهِمَ مَعْدُودَةٍ وَكَانُوا۟ فِيهِ مِنَ ٱلزَّٰهِدِينَ
Kuma suka sayar[1] da shi da 'yan kuɗi kaɗan, dirhamõmi ƙidãyayyu, Kuma sun kasance, a wurinsa, daga mãsu isuwa da abu kaɗan.
[1] Ãyarin, sun tafi da shi, sun sayar da shi a kan kuɗi kaɗan, dõmin sun sani, shĩ bã bãwansu ba ne, tsintõ shi suka yi. Sabõda haka kõme suka sãmu game da shi, rĩba ce a gare su. Kuma gudun kada iyãyensa su gãne shi, su rasa kõme daga gare shi gabã ɗaya.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net