Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 12 · Aya ta 108

Yusuf 12:108

يوسف

قُلْ هَـٰذِهِۦ سَبِيلِىٓ أَدْعُوٓا۟ إِلَى ٱللَّهِ ۚ عَلَىٰ بَصِيرَةٍ أَنَا۠ وَمَنِ ٱتَّبَعَنِى ۖ وَسُبْحَـٰنَ ٱللَّهِ وَمَآ أَنَا۠ مِنَ ٱلْمُشْرِكِينَ

Ma’ana

Ka ce: "Wannan ce hanyãta;[1] inã kira zuwa ga Allah a kan basĩra, nĩ da waɗanda suka bĩ ni, kuma tsarki ya tabbata ga Allah! Nĩ kuma, ban zama daga mãsu shirki ba."

[1] Bin hukuncin Allah kamar yadda ƙissar Yũsufu ta nũna cewa, a ƙõwane hãli mutum ya kasance akwai yadda Allah Ya yi umurni a wannan hãlin da a bĩ Shi, wanda ya bi umurnin Allah, to, zai ɗaukaka a dũniya kuma Allah bã zai tõzartar da lãdarsa a Lãhira ba.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Yusuf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net