Yusuf 12:100
يوسفوَرَفَعَ أَبَوَيْهِ عَلَى ٱلْعَرْشِ وَخَرُّوا۟ لَهُۥ سُجَّدًا ۖ وَقَالَ يَـٰٓأَبَتِ هَـٰذَا تَأْوِيلُ رُءْيَـٰىَ مِن قَبْلُ قَدْ جَعَلَهَا رَبِّى حَقًّا ۖ وَقَدْ أَحْسَنَ بِىٓ إِذْ أَخْرَجَنِى مِنَ ٱلسِّجْنِ وَجَآءَ بِكُم مِّنَ ٱلْبَدْوِ مِنۢ بَعْدِ أَن نَّزَغَ ٱلشَّيْطَـٰنُ بَيْنِى وَبَيْنَ إِخْوَتِىٓ ۚ إِنَّ رَبِّى لَطِيفٌ لِّمَا يَشَآءُ ۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلْعَلِيمُ ٱلْحَكِيمُ
Kuma ya ɗaukaka iyãyensa biyu a kan karaga, sa'an nan suka fãɗi a gare shi, suna mãsu sujada.[1] Kuma ya ce: "Ya bãbãna! Wannan ita ce fassarar mafarkin nan nãwa. Lalle ne Ubangijina Ya sanya shi ya tabbata sõsai, kuma lalle ne Ya kyautata game da ni a lõkacin da Ya fitar da ni daga kurkuku. Kuma Ya zo da ku daga ƙauye, a bãyan Shaiɗan yã yi fisgar ɓarna a tsakãnĩna da tsakãnin 'yan'uwana, Lalle ne Ubangijina Mai tausasawa ne ga abin da Yake so. Lalle ne Shĩ, Shĩ ne Masani, Mai hikima."
[1] Sujada idan ta zama da umurnin Allah ne ga kõwa, to, ba ta da laifi duk yadda take, amma idan an yi ta bã inda Allah Ya ajiye ta ba, to, tã zama kãfirci. A Musulunci gaisuwa da dũƙãwar kai haram ce, waɗansu Malamai sun ce idan ba ta kai ga rukũ'i ba, makarũhi ce, amma idan ta kai ga rukũ'i tã zama harãmun ga duka mãlamai, wãtau ijmã'in Malamai sun haramta dũƙãwar da ta kai ga rukũ'i.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net