Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 11 · Aya ta 84

Hud 11:84

هود

وَإِلَىٰ مَدْيَنَ أَخَاهُمْ شُعَيْبًا ۚ قَالَ يَـٰقَوْمِ ٱعْبُدُوا۟ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَـٰهٍ غَيْرُهُۥ ۖ وَلَا تَنقُصُوا۟ ٱلْمِكْيَالَ وَٱلْمِيزَانَ ۚ إِنِّىٓ أَرَىٰكُم بِخَيْرٍ وَإِنِّىٓ أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ مُّحِيطٍ

Ma’ana

Kuma zuwa ga Madyana (Mun aika) ɗan'uwansu[1] Shu'aibu. Ya ce: "Ya Mutãnena! Ku bauta wa Allah. Ba ku da wani abin bautãwa fãce shi kuma kada ku rage mũdu da sikẽli. Lalle nĩ, inã ganin ku da wadãta[2]. Kuma lalle inã ji muku tsõron azãbar yini mai kẽwayẽwa."

[1] Lãrabãwa ne, sunã zaune a tsakãnin Hijaz da Shãm.
[2] Inã ganin ku a cikin wadãta; bã ku da bukãtar rage wa mutãne kãyansu. Sabõda haka ku yi adalci ga mutãne wajen ciniki ya fi muku alheri daga dũkiyar haram mai ƙãrewa kõme yawanta.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Hud

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net