Hud 11:115
هودوَٱصْبِرْ فَإِنَّ ٱللَّهَ لَا يُضِيعُ أَجْرَ ٱلْمُحْسِنِينَ
Kuma ka yi haƙuri. Allah bã Ya tõzartar da lãdar mãsu kyautatãwa.[1]
[1] Haƙuri a kan ibãda wãjibi ne, haka kuma kyautatãwa, wãtau shĩ ne yin kõwãne aiki na ibãda tsantsa kamar salla kõ na ma'amala kamar ciniki da aure, dõmĩn Allah kawai. An yi wa wannan fanni na biyu sũna da "Tasawwuf", bidi'a ne dõmin bai taho daga sunna ba. Asalinsa "theosophy" daga lugar Ajam, ma'anarsa neman hikima ta Allah a hãlin keɓance kai a cikin kaɗaita da wasu aikace-aikace na ibada, kamar girka ga 'yanbõri.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net