Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 11 · Aya ta 112

Hud 11:112

هود

فَٱسْتَقِمْ كَمَآ أُمِرْتَ وَمَن تَابَ مَعَكَ وَلَا تَطْغَوْا۟ ۚ إِنَّهُۥ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ

Ma’ana

Sai ka daidaitu[1] kamar yadda aka umurce ka, kai da waɗanda suka tũba tãre da kai kunã bã mãsu ƙẽtara haddi ba. Lalle shĩ, Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.

[1] Wannan ãyã tanã hana dukan bidi'a a cikin addini. Tun da ba a yarda Annabi ya ƙara ra'ayinsa ba sai dai ya bi umurnin Allah kamar yadda Ya yi umurnin, kuma haka ne Ya umurci wanda ya bi Annabi. Sabõda haka mai sãɓa wa umurnin Allah da ƙãri ko ragi, bã ya cikin mabiyan Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Hud

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net