Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 10 · Aya ta 98

Yunus 10:98

يونس

فَلَوْلَا كَانَتْ قَرْيَةٌ ءَامَنَتْ فَنَفَعَهَآ إِيمَـٰنُهَآ إِلَّا قَوْمَ يُونُسَ لَمَّآ ءَامَنُوا۟ كَشَفْنَا عَنْهُمْ عَذَابَ ٱلْخِزْىِ فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا وَمَتَّعْنَـٰهُمْ إِلَىٰ حِينٍ

Ma’ana

To, dõmin me wata alƙarya ba ta kasance ta yi[1] ĩmãniba har ĩmãninta ya amfãne ta, fãcemutãnen Yũnus? A lõkacin da suka yi ĩmãni, Munjanye Azãbar wulãkanci daga gare su a cikin rãyuwar dũniya. Kuma Muka jiyar da su dãɗi zuwa wani lõkaci.

[1] Alƙaryun da aka aika da Manzanni cikinsu, ba su yi ĩmãni duka ba fãce mutum ɗaya, kõ biyu a gabãnin halaka ta sãmi mutãnensu. Sai dai alƙaryar Yũnusa, ita kam tã ji tsõro, ta yi ĩmãni a gabãnin saukar azãba, sabõda haka suka tshĩra, ba a halaka garin bawatau Nĩnawa. Watau bãbu mai iya sãmun ĩmãni sai Allah Ya nufe shi da haka. Kõ da mai yin gargaɗin ya kan yiwu ya karkace, sai da tsarin Allah.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Yunus

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net