Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 10 · Aya ta 62

Yunus 10:62

يونس

أَلَآ إِنَّ أَوْلِيَآءَ ٱللَّهِ لَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ

Ma’ana

To, Lalle ne masõyan[1] Allah bãbu tsõro a kansu, kuma bã zã su kasance sunã yin baƙin ciki ba.

[1] Waliyyin Allah, shi ne masõyin Allah da sharaɗin ya zama mumini mai taƙawa watau yanã aiki da abin da Allah Ya umurce shi, kuma yanã barin abin da Allah Ya hana shi, bisa harshen Annabinsa wanda yake biya. Bãbu ƙarin kõme bãbu ragi. Bushãrarsu, ita ce yabon mutãne a gare su, kõ kuma a lõkacin mutuwarsu malã'iku su riƙa yi musu bushãra da gamuwa da Ubangijinsu, kõ kuma a cikin kabari wajen tambaya. Allah ne Mafi sani.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Yunus

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net