Daga Abu Sa'id AlKudri ya ce: Mu'awiya ya fito ga wata halƙa a cikin masallaci, sai ya ce: Me ya zaunar da ku? suka ce: Mun zauna muna ambatan Allah, ya ce kun rantse da Allah babu abinda ya zaunar da ku sai hakan? suka ce: Wallahi babu abinda ya zaunar da mu sai hakan, ya ce: Amma ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku, kuma babu wani a matsayina daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mafi ƙarancin hadisi daga gareni: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fito ga wata halƙa daga sahabbansa, sai ya ce; "Me ya zaunar da ku?" suka ce: Mun zauna muna ambatan Allah muna gode masa akan abinda ya shiryar da mu na musulunci, kuma ya yi baiwa da shi garemu, ya ce: "Kun rantse da Allah babu abinda ya zaunar da ku sai hakan? suka ce: Wallahi babu abinda ya zaunar da mu sai hakan, ya ce: "Amma ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku, sai dai cewa (Mala'ika) Jibril ya zo min sai ya ba ni labarin cewa Allah - mai girma da ɗaukaka - Yana yi wa mala'iku alfahari da ku".
Tushen bai rubuta wata daraja ga wannan ruwaya ba.
Inda Insakulofidiyar Hadisan Annabi da aka Fassara (HadeethEnc.com) take da ainihin rubutun wata ruwaya, ana nuna fassararta a ƙarƙashin wannan ruwayar tare da sunan tushen. An haɗa su biyun ne ta hanyar shiri, daga Larabcin kaɗai: dukan rubutun hadisin da ke cikin insakulofidiyar, tare da sunan Sahabin da ya ambata, shi ne ƙarshen ruwayar harafi da harafi. Babu wanda ya bincika wannan haɗin, kuma masu bitar Sabīl ba su duba fassarar ba. Larabcin shi ne rubutun.
Rubutun Larabci, lambobi, sunayen littattafai da darajoji ana nuna su daidai yadda suke a cikin wani buɗaɗɗen tarin bayanai (hadith-api). Sabīl bai tabbatar da daidaitonsa ko haƙƙoƙinsa ba tukuna, kuma ba a fara bitar malamai a kansa ba. Kafin lokacin, ku kwatanta ruwaya da bugaggen littafi kafin ku dogara da ita.