Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yayewa wani mumini wani baƙin ciki daga baƙin cikin duniya Allah Zai yaye masa wani baƙin ciki daga baƙin cikin ranar alƙiyama, wanda ya yalwatawa wanda yake cikin matsuwa to Allah Zai yalwata masa a duniya da lahira, wanda ya suturta wani musulmi Allah Zai suturta shi a duniya da lahira, Allah Yana cikin taimakon bawa matuƙar bawan yana cikin taimakon ɗan'uwansa, wanda ya bi wata hanya yana neman Ilimi a cikinta to Allah Zai sawwaƙe masa hanyar shiga aljanna da ita, kuma wasu mutane basu taru ba a wani ɗaki daga cikin ɗakunan Allah suna karanta littafin Allah kuma suna dirasarsa a tsakaninsu sai nutsuwa ta saukar musu, kuma rahama ta lullubesu, mala'iku sun kewayesu, kuma Allah Ya ambacesu a cikin wadanda ke tare da shi, wanda aikinsa ya jinkirtar da shi to nasabarsa bazata gaggauto da shi ba".
Tushen bai rubuta wata daraja ga wannan ruwaya ba.
Inda Insakulofidiyar Hadisan Annabi da aka Fassara (HadeethEnc.com) take da ainihin rubutun wata ruwaya, ana nuna fassararta a ƙarƙashin wannan ruwayar tare da sunan tushen. An haɗa su biyun ne ta hanyar shiri, daga Larabcin kaɗai: dukan rubutun hadisin da ke cikin insakulofidiyar, tare da sunan Sahabin da ya ambata, shi ne ƙarshen ruwayar harafi da harafi. Babu wanda ya bincika wannan haɗin, kuma masu bitar Sabīl ba su duba fassarar ba. Larabcin shi ne rubutun.
Rubutun Larabci, lambobi, sunayen littattafai da darajoji ana nuna su daidai yadda suke a cikin wani buɗaɗɗen tarin bayanai (hadith-api). Sabīl bai tabbatar da daidaitonsa ko haƙƙoƙinsa ba tukuna, kuma ba a fara bitar malamai a kansa ba. Kafin lokacin, ku kwatanta ruwaya da bugaggen littafi kafin ku dogara da ita.