Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sahih Muslim

Lamba 6525

Lamba 6525Littafi na 45, lamba 25Lambar Larabci 2558.01
حَدَّثَنِي مُحَمَّدُ بْنُ الْمُثَنَّى، وَمُحَمَّدُ بْنُ بَشَّارٍ، - وَاللَّفْظُ لاِبْنِ الْمُثَنَّى - قَالاَ حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ جَعْفَرٍ، حَدَّثَنَا شُعْبَةُ، قَالَ سَمِعْتُ الْعَلاَءَ بْنَ عَبْدِ الرَّحْمَنِ، يُحَدِّثُ عَنْ أَبِيهِ، عَنْ أَبِي، هُرَيْرَةَ أَنَّ رَجُلاً، قَالَ يَا رَسُولَ اللَّهِ إِنَّ لِي قَرَابَةً أَصِلُهُمْ وَيَقْطَعُونِي وَأُحْسِنُ إِلَيْهِمْ وَيُسِيئُونَ إِلَىَّ وَأَحْلُمُ عَنْهُمْ وَيَجْهَلُونَ عَلَىَّ ‏.‏ فَقَالَ ‏ "‏ لَئِنْ كُنْتَ كَمَا قُلْتَ فَكَأَنَّمَا تُسِفُّهُمُ الْمَلَّ وَلاَ يَزَالُ مَعَكَ مِنَ اللَّهِ ظَهِيرٌ عَلَيْهِمْ مَا دُمْتَ عَلَى ذَلِكَ ‏"‏ ‏.‏
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum ya ce: Ya manzon Allah, ina da wasu 'yan uwa ina sadar musu (da zumunci), su kuma suna yanke mini, ina kyautata musu, su suna munanawa a gareni, ina haƙuri da su, su kuma suna yi min wauta, sai ya ce: "Idan ka kasance kamar yadda ka faɗa, to, kamar kana cusa musu toka mai zafi ne a bakin su, kuma wani mai rinjaye a kansu daga Allah ba zai gushe tare da kai ba muddin dai ka kasance a kan haka".

Fassara: HadeethEnc.comSharhinsa

Tushen bai rubuta wata daraja ga wannan ruwaya ba.

Inda Insakulofidiyar Hadisan Annabi da aka Fassara (HadeethEnc.com) take da ainihin rubutun wata ruwaya, ana nuna fassararta a ƙarƙashin wannan ruwayar tare da sunan tushen. An haɗa su biyun ne ta hanyar shiri, daga Larabcin kaɗai: dukan rubutun hadisin da ke cikin insakulofidiyar, tare da sunan Sahabin da ya ambata, shi ne ƙarshen ruwayar harafi da harafi. Babu wanda ya bincika wannan haɗin, kuma masu bitar Sabīl ba su duba fassarar ba. Larabcin shi ne rubutun.

Littafi na 45 · The Book of Virtue, Enjoining Good Manners, and Joining of the Ties of Kinship

Rubutun Larabci, lambobi, sunayen littattafai da darajoji ana nuna su daidai yadda suke a cikin wani buɗaɗɗen tarin bayanai (hadith-api). Sabīl bai tabbatar da daidaitonsa ko haƙƙoƙinsa ba tukuna, kuma ba a fara bitar malamai a kansa ba. Kafin lokacin, ku kwatanta ruwaya da bugaggen littafi kafin ku dogara da ita.