Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya faɗa a ranar Khaibara: "Zan bada wannan tutar ga wani mutum mai ƙaunar Allah da ManzonSa, Allah zai yi buɗi ta hannayensa" Umar ɗan Khaɗɗab ya ce: Ban so shugabanci ba sai wannan ranar, ya ce sai na yi ɗigirgire saboda ita dan kwaɗayin a kirawoni gareta, ya ce: Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kira Aliyu bin Abi Ɗalib - Allah Ya yarda da shi -, sai ya ba shi ita, ya ce: "Ka tafi, kada ka juya, har sai Allah Ya buɗe maka." Ya ce sai Aliyu ya tafi ɗan wani taku, sannan ya tsaya bai juya ba, sai ya yi magana: Ya Manzon Allah, akan me zan yaƙi mutane? Ya ce: "Ka yaƙesu har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammad manzon Allah ne, idan suka aikta hakan to hakika sun hana jinanensu da dukiyoyinsu daga gareni sai da hakkinsu kuma hisabinsu yana ga Allah".
Tushen bai rubuta wata daraja ga wannan ruwaya ba.
Inda Insakulofidiyar Hadisan Annabi da aka Fassara (HadeethEnc.com) take da ainihin rubutun wata ruwaya, ana nuna fassararta a ƙarƙashin wannan ruwayar tare da sunan tushen. An haɗa su biyun ne ta hanyar shiri, daga Larabcin kaɗai: dukan rubutun hadisin da ke cikin insakulofidiyar, tare da sunan Sahabin da ya ambata, shi ne ƙarshen ruwayar harafi da harafi. Babu wanda ya bincika wannan haɗin, kuma masu bitar Sabīl ba su duba fassarar ba. Larabcin shi ne rubutun.
Rubutun Larabci, lambobi, sunayen littattafai da darajoji ana nuna su daidai yadda suke a cikin wani buɗaɗɗen tarin bayanai (hadith-api). Sabīl bai tabbatar da daidaitonsa ko haƙƙoƙinsa ba tukuna, kuma ba a fara bitar malamai a kansa ba. Kafin lokacin, ku kwatanta ruwaya da bugaggen littafi kafin ku dogara da ita.