Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wanda ya mari kunci, kuma ya yaga aljihuna, kuma ya yi ihu irin ta Jahiliyya to ba shi tare da mu

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بنِ مَسْعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَيْسَ مِنَّا مَنْ لَطَمَ الخُدُودَ، وَشَقَّ الجُيُوبَ، وَدَعَا بِدَعْوَى الجَاهِلِيَّةِ».
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya mari kunci, kuma ya yaga aljihuna, kuma ya yi ihu irin ta Jahiliyya to ba shi tare da mu".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani kuma ya tsoratar akan wasu ayyukan mutanen Jahiliyya, sai ya ce: Ba ya tare da mu: Na farko: Wanda ya mari kundukuki (kumatu) an keɓanci kundukuki dan kasancewarsa shi ne galibi a hakan, inba haka ba marin sauran fuska yana shiga cikin hanin. Na biyu: Yaga abnida ake buɗewa daga tufa dan kai ya shiga cikinsa saboda tsananin baƙin ciki. Na uku: Yin kururuwa irin ta mutanen Jahiliyya kamar ihu da kaico da halaka da kukan mutuwa da wanin hakan.

Fa’idoji
  1. Wannan narkon a cikin hadisin yana nuni akan cewa waɗannan ayyukan suna daga cikin manyan zunubai.
  2. Wajabcin haƙuri akan masifa, da haramta fushi akan ƙaddarorin Allah masu raɗaɗi, da bayyanar da hakan: Da kukan mutuwa ko aske kai ko yaga riga ko wanin hakan.
  3. Haramcin kwaikwayon Jahiliyya da al'amuransu waɗanda mai shari'antawa bai tabbatar da su ba.
  4. Babu laifi akan damuwa da hawaye, shi ba ya kore haƙuri akan hukuncin Allah - Maɗaukakin sarki -, kawai shi tausayi ne Allah Ya sanya shi a cikin zukatan makusanta da masoya.
  5. Yarda da hukuncin Allah ya wajaba akan musulmi, idan bai yarda ba to haƙuri wajibi ne a kansa.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 81) (1294). صحيح مسلم (1/ 99) (103). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص287). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (2/ 379) .

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
MAS'ALOLIN JAHILIYYA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com