Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lallai kana da abin da ka yi burin da kwatankwacin sa tare da shi

عَن أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنهُ عَنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِنَّ أَدْنَى مَقْعَدِ أَحَدِكُمْ مِنَ الْجَنَّةِ أَنْ يَقُولَ لَهُ: تَمَنَّ فَيَتَمَنَّى، وَيَتَمَنَّى، فَيَقُولُ لَهُ: هَلْ تَمَنَّيْتَ؟ فَيَقُولُ: نَعَمْ، فَيَقُولُ لَهُ: فَإِنَّ لَكَ مَا تَمَنَّيْتَ وَمِثْلَهُ مَعَهُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce : «Lallai mafi ƙankantar matsayin ɗayanku a cikin aljanna shi ne Ya ce masa: Ka yi buri, sai ya yi buri, kuma ya yi buri, sai Ya ce da shi: Shin ka yi burin kuwa? sai ya ce: Eh, sai Ya ce da shi: Lallai kana da abin da ka yi burin da kwatankwacin sa tare da shi».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi ƙanƙantar matsayi da daraja ga wanda ya shiga aljanna shi ne Ya ce da shi: Ka yi buri, sai ya yi buri, kuma ya yi buri, har sai ya zama babu wani burin da zai rage masa sai ya ambace shi , sai Ya ce masa: Shin ka yi burin kuwa? sai ya ce: Eh, sai Ya ce masa: To lallai kana da abinda ka yi burin dama kwatankwacinsa tare da shi.

Fa’idoji
  1. Fifikon matsayin 'yan aljanna.
  2. Bayanin girman karamcin Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -.
  3. Ni'imar aljanna ba ta taƙaituwa akan wani ayyanannen abu, kai mumini zai samu dukkan abinda yake burinsa kuma ransa yake sha'awarsa dan falala da kyauta da kuma karamci daga Allah - Maɗaukakin sarki -.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 167) (182). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (9/ 3585). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص1090). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (3/ 348). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1292).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
RAYUWAR LAHIRA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com