Sahabbai sun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wani dare sai ya dubi wata - daren goma sha hudu -, sai ya ce: Lallai muminai za su ga Ubanbijinsu a hakika da ido ba tare da wani rikici ba, kuma cewa su ba za su yi cunkoso ba, kuma wahala ba zata samesu ba ko tsanani a yayin ganinsa - Madaukakin sarki -. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Idan kuna da ikon yanke abubuwan da zasu hana ku sallar Asuba da sallar La'asar to ku aikata, ku zo da su (Sallolin) a cike a lokacinsu a cikin jama'a, domin cewa hakan yana daga sabubban gani zuwa fuskar Allah - Mai girma da daukaka -, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya karanta ayar: {Ka tsarkake da godiyar Ubangijinka kafin bullowar rana da kafin faduwarta}.
- Bushara ga masu imani da ganin Allah - Madaukakin sarki - a aljanna.
- Daga hanyoyin Da'awa: Karfafawa da kwadaitarwa da buga misalai.
صحيح البخاري (1/ 115) (554)، (6/ 139) (4851). صحيح مسلم (1/ 439) (633). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 259). تذكرة المؤتسي شرح عقيدة الحافظ عبد الغني المقدسي، لعبدالرزاق البدر (ص177). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 734). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (2/ 776). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (13/ 271). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص1091).