Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

‌Za'a tashi mutane a ranar Lahira marasa takalma tsirara kuma marasa kaciya

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمنين رَضيَ اللهُ عنها قَالَتْ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «يُحْشَرُ النَّاسُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ حُفَاةً عُرَاةً غُرْلًا» قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ النِّسَاءُ وَالرِّجَالُ جَمِيعًا يَنْظُرُ بَعْضُهُمْ إِلَى بَعْضٍ؟ قَالَ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «يَا عَائِشَةُ، الْأَمْرُ أَشَدُّ مِنْ أَنْ يَنْظُرَ بَعْضُهُمْ إِلَى بَعْضٍ».
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: «‌Za'a tashi mutane a ranar Lahira marasa takalma tsirara kuma marasa kaciya». Na ce: Ya Manzon Allah! mata da maza baki ɗaya sashinsu yana kallon sashi? Sai (Manzon Allah) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «‌Ya A'isha, al'amarin ya fi tsanani a ce sashinsu yana kallon sashi».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya siffanta sashin abinda ke cikin ranar alƙiyama, kuma mutane za'a tarasu bayan tashinsu daga ƙaburburansu dan yin hisabi, kuma cewa halinsu zasu zama marasa takalma, tsirara babu tufafi, marasa kaciya kamar ranar da iyayensu suka haifesu, yayin da Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ji hakan sai ta ce tana mai mamaki: Ya Manzon Allah ! maza da mata baki ɗayansu sashinsu yana kallon sashi?! Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa: Sha'anin tsayuwar da taruwa bayan tashi daga mutuwa a cikinsa akwai tsorace-tsoracen da zai ɗauke hankalin mutane da idanuwansu daga kallan al'aurori.

Fa’idoji
  1. Bayanin tsorace-tsoracen ranar Lahira, kuma cewa mutum a wannan ranar wani abu ba zai shagaltar da shi daga hisabinsa ba haka nan ayyukansa.
  2. Karfafawa cewa mutum ba zai afka cikin saɓo ba sai dai a halin rafkana; dan da zai tina girman wanda ya saɓawa ko uƙubarSa da bai rafkana ba daga tinaShi da kuma gode maSa da kyakkyawan bautarSa ko da ƙiftawar ido, saboda haka zaka ga ma'abota taron alƙiyama sun shagalta da kawunansu sashinsu ba ya kallon sashi.
  3. Tsananin kunyar mata a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, wannan Nana A'isha ce - Allah Ya yarda da ita - tana tambaya cikin kunya lokacin da ta ji cewa za'a tashi halitta tsirara maza da mata.
  4. Sindi ya ce: Kowanne mutum ya shagalta da al'amarinsa kuma bai san halin ɗan'uwansa ba, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kowane mutum daga cikinsu a wannan ranar sha'aninsa ya wadace shi} [Abasa: 37]. Babu wani da zai iya juyawa zuwa ga al'aurar wani.
  5. Kaciya: Ita ga namiji ita ce: Yanke fatar da ta rufe hashafa, ta mace kuma ita ce: Yanke fatar da ke saman bigiren da azzakari yake shiga ya yi kama da ƙahon zakara.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 109) (6527). صحيح مسلم (4/ 2194) (2859). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 373). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 302). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 483). المعجم الوسيط، (2/ 651).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
RAYUWAR LAHIRA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com