Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Diga-digan bawa ba za su gusheba a ranar Alkiyama har sai an tambaye shi game da rayuwarsa a me ya karar da ita, da kuma iliminsa me ya aikata da shi, da dukiyarsa daga ina ya samota kuma a me ya ciyar da ita, da jikinsa wanne aiki ya yi da shi

عَنْ أَبِي بَرْزَةَ الأَسْلَمِيِّ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا تَزُولُ قَدَمَا عَبْدٍ يَوْمَ القِيَامَةِ حَتَّى يُسْأَلَ عَنْ عُمُرِهِ فِيمَا أَفْنَاهُ، وَعَنْ عِلْمِهِ فِيمَ فَعَلَ، وَعَنْ مَالِهِ مِنْ أَيْنَ اكْتَسَبَهُ وَفِيمَ أَنْفَقَهُ، وَعَنْ جِسْمِهِ فِيمَ أَبْلَاهُ».
Daga Abu Burzata Al-Aslami - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce : "Diga-digan bawa ba za su gusheba a ranar Alkiyama har sai an tambaye shi game da rayuwarsa a me ya karar da ita, da kuma iliminsa me ya aikata da shi, da dukiyarsa daga ina ya samota kuma a me ya ciyar da ita, da jikinsa wanne aiki ya yi da shi".
Tirmizi ne ya ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wani mutum daga mutane da zai ketare matsayar hisabi a ranar Alkiyama zuwa aljanna ko wuta ba har sai an tambaye shi game da wasu al'amura: Na daya: Rayuwarsa a me ya karar da ita? Na biyu: Iliminsa shin ya neme shi ne saboda Allah? kuma ya yi aiki da shi? kuma shin ya isar da shi ga wanda ya cancance shi? Na uku: Dukiyarsa daga ina ya samota shin daga halal ne ko daga haram? kuma a me ya ciyar da ita a abinda zai yardar da Allah ne, ko a abinda zai fusatar da Shi? Na hudu: Jikinsa da karfinsa da lafiyarsa da samartakarsa a me ya yi da shi ya kuma aiwatar da shi?

Fa’idoji
  1. Kwadaitarwa akan ribar rayuwa a cikin abinda zai yardar da Allah - Madaukakin sarki -.
  2. Ni'imomin Allah ga bayinSa masu yawa ne kuma za'a tambaye shi daga ni'imar da ya kasance a cikinta, to ya wajaba akansa ya sanya ni'imomin Allah a abinda zai yardar da Shi.
Madogara

سنن الترمذي (4/ 217) (2417). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 371). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 478). المعجم الوسيط (2/ 704).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
RAYUWAR LAHIRA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com