Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Shin ba zan baku labarin 'yan aljanna ba? Duk mai rauni da ake rainawa, da zai rantse da Allah zai kuɓutar da shi, shin ba zan baku labarin 'yan wuta ba? duk mai ƙaton ciki mai kaushin rai mai girman kai

عَنْ حَارِثَةَ بْنِ وَهْبٍ الخُزَاعِيِّ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «أَلاَ أُخْبِرُكُمْ بِأَهْلِ الجَنَّةِ؟ كُلُّ ضَعِيفٍ مُتَضَعِّفٍ، لَوْ أَقْسَمَ عَلَى اللَّهِ لَأَبَرَّهُ، أَلاَ أُخْبِرُكُمْ بِأَهْلِ النَّارِ: كُلُّ عُتُلٍّ جَوَّاظٍ مُسْتَكْبِرٍ».
Daga Harisa ɗan Wahb alKhuza'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Shin ba zan baku labarin 'yan aljanna ba? Duk mai rauni da ake rainawa, da zai rantse da Allah zai kuɓutar da shi, shin ba zan baku labarin 'yan wuta ba? duk mai ƙaton ciki mai kaushin rai mai girman kai".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin sashin siffofin 'yan aljanna da 'yan wuta. Mafi yawancin 'yan aljanna sune: "Dukkan mai rauni mai ƙanƙar da kai", wato: Mai ƙanƙan da kai mai ƙanƙanr da kai ga Allah - Maɗaukakin sarki -, mai ƙasƙantar da kansa gareShi, har takai wasu daga mutane suna raunana shi kuma suna wulaƙanta shi, wannan mai ƙasƙantar da kai ga Allah - Maɗaukakin sarki - da zai yi rantsuwa da Allah dan kwaɗayi a cikin karamcin Allah - Maɗaukakin sarki -, da Allah Ya kuɓutar da shi, kuma Ya tabbatar masa da abinda ya yi rantsuwa akansa kuma Ya amsa buƙatarsa da addu'arsa. Kuma mafi yawancin 'yan wuta su ne: Dukkan "Mai ƙaton ciki" shi ne mai kaushin zuciya, mai bushewar zuciya mai tsananin husuma, ko mai alfasha wanda ba ya jawuwa ga alheri, "Mai yawan girman kai" shi ne mai girman kai, mai yawan ci, mai ƙiba, mai taƙama a tafiyarsa, mai mummunar ɗabi'a, "Mai girman kai" saboda butulcewarsa ga gaskiya, da kuma wulaƙanta waninsa.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa akan siffantuwa da siffofin 'yan aljanna, da kuma gargaɗarwa daga siffofin 'yan wuta.
  2. Kanƙantar da kai yana kasancewa ne ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da umarninSa da haninSa, da jawuwa garesu, kuma yana kasancewa ne ga halitta da rashin yi musu girman kai.
  3. Ibnu Hajar ya ce: Abin nufi cewa mafi yawancin 'yan aljanna sune waɗannan, kamar yadda mafi yawancin 'yan wuta sune ɗaya ɓangaren, bawai abin nufi shi ne gamewa a ɓangarori biyun ba.
Madogara

صحيح البخاري (6/ 159) (4918). صحيح مسلم (4/ 2190) (2853). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (5/ 5). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 47). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 340). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 264).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
RAYUWAR LAHIRA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com