Daga Mu'awiya -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Ladanai sune mafiya tsawon wuyaye a ranar alƙiyama".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa ladanai waɗanda suke kiran sallah sune mafiya tsawon wuyaye a cikin mutane ranar alƙiyama, saboda girman aikinsu, da kuma yawan alherinsu, da girman ladansu.
Fa’idoji
Falalar kiran sallah da kwaɗaitarwa a cikinsa.
Bayanin matsayin ladanai da ɗaukakar matsayinsu a ranar alƙiyama.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 290) (387).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 251).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 31).
شرح صحيح مسلم، النووي (4/ 89).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 768).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com