Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Idan aka tambayi musulmi a cikin ƙabari: Yana shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad manzon Allah ne

عَنِ البَرَاءِ بْنِ عَازِبٍ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «المُسْلِمُ إِذَا سُئِلَ فِي القَبْرِ: يَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ»، فَذَلِكَ قَوْلُهُ: {يُثَبِّتُ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا بِالقَوْلِ الثَّابِتِ فِي الحَيَاةِ الدُّنْيَا وَفِي الآخِرَةِ} [إبراهيم: 27].
Daga Bara'u ɗan Azib - Allah Ya yarda da shi - manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan aka tambayi musulmi a cikin ƙabari: Yana shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad manzon Allah ne". to wannan shi ne faɗinSa: {Allah Yana tabbatar wa waɗanda suka yi imani da faɗa tabbatacciya a cikin rayuwar duniya da kuma lahira} [Ibrahim: 27].
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Za'a tambayi mumini a cikin ƙabari, sai mala'iku biyu waɗanda aka wakilta da hakan su tambaye shi su ne Munkar da Nakir, kamar yadda ambatansu ya zo a Hadisai masu yawa, sai ya shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah , kuma cewa (Annabi) Muhammad manzon Allah ne, Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: wannan shi ne tabbatacciyar magana wacce Allah Ya faɗa a cikinta: {Allah Yana tabbatar da wadanda su ka yi imani da magana matabbaciya a rayuwar duniya da kuma a lahira} [Ibrahim: 27].

Fa’idoji
  1. Lallai cewa tambayar ƙabari gaskiya ne.
  2. Falalar Allah ga bayinSa muminai a duniya da lahira ta hanyar tabbatar da su akan tabbatacciyar magana.
  3. Falalar shaidawa da Tauhidi da mutuwa akan hakan.
  4. Tabbatar war Allah ga mumini a duniya da tabbata akan imani, da shiga hanya madaidaiciya, a lokacin mutuwa kuma da mutuwa akan Tauhidi, a ƙabari a lokacin tambayar mala'iku biyu.
Madogara

صحيح البخاري (6/ 80) (4699). صحيح مسلم (4/ 2201) (2871). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 498). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 386).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
RAYUWAR BARZAHU

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com