Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

An kirawo shi ne da Alkidr saboda ya zauna akan wata Qasa Busashiya fara, sai kawai ta riqa motsi a bayansa ta koma koriya

عن أبي هريرة رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «إنَّما سُمِّيَ الخَضِرُ أنَّه جلس على فَرْوَة بيضاء، فإذا هي تهتزُّ مِنْ خَلْفِه خَضْراء».
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi daga Annabi SAW ya ce: "An kirawo shi ne da Alkidr saboda ya zauna akan wata Qasa Busashiya fara, sai kawai ta riqa motsi a bayansa ta koma koriya"
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi yana bada labarin cewa An kirawo shi ne da Alkidr saboda ya zauna akan wata Qasa Busashiya fara, sai kawai ta riqa motsi a bayansa ta koma koriya, saboda abunda ya futo a cikinta na ciyayi da koren ganye, Maganarsa a zo cikin Qur'ani a cikin Qissar Annabi Musa a Suratu Alkahf, kuma Malamai sunyi savani kan cewa wai shi Annabi ne ko kuma Waliyyi ne bawan Allah, zance mafi inganci Annabi ne

Madogara

- صحيح البخاري، نشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422ه. - كشف المشكل من حديث الصحيحين، لجمال الدين أبي الفرج عبد الرحمن بن علي بن محمد الجوزي، المحقق: علي حسين البواب، الناشر: دار الوطن – الرياض. - إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري، لأحمد بن محمد بن أبى بكر بن عبد الملك القسطلاني القتيبي المصري، الناشر: المطبعة الكبرى الأميرية، مصر، الطبعة: السابعة، 1323 هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ANNABAWA DA MANZANNI MAGABATA AMINCI A GARESU

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com