Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Manzon Allah SAW yayi Maka Istigfari? ya ce: Ey, haka ma kai sannan ya karanta wannan Ayar: "Kuma ka nemi gafarar zunubanka da kuma Muminai Maza da Mata"

عن عبد الله بن سَرْجس، قال: رأيتُ النبي صلى الله عليه وسلم وأكلتُ معه خُبْزا ولحْمًا، أو قال ثَرِيدًا، قال فقلتُ له: أَسْتَغْفَرَ لك النبي صلى الله عليه وسلم ؟ قال: نعم، ولك، ثم تَلا هذه الآية {وَاسْتَغْفِرْ لِذَنْبِكَ وَلِلْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ} [محمد: 19] قال: ثم دُرْتُ خَلْفَه فنَظَرْتُ إلى خاتَم النُّبوة بين كَتِفَيْه، عند ناغِض كَتِفِه اليُسْرى، جُمْعًا، عَلَيْه خِيلانٌ كأمْثال الثَّآلِيلِ.
Daga Abdullahi Bn Sarjis, ya ce: naga Manzon Allah SAW kuma muka ci Gurasa da Nama tare da shi, ko kuma ya ce: Tharid, ya ce: sai na ce da shi: Manzon Allah SAW yayi Maka Istigfari? ya ce: Ey, haka ma kai sannan ya karanta wannan Ayar: "Kuma ka nemi gafarar zunubanka da kuma Muminai Maza da Mata" [Muhammad" ya ce: sannan na kewa bayansa sai naga Hatimin Annabta a tsakanin Kafaxunsa, a gefen Kafaxarsa na Hagu, kamar dunqulen hannu, akansa tabo, Kamar qwan tattabara
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Babban Sahabin Annabi Abdullahi Bn Sarjis yana cewa: cewa shi yaga Manzon Allah SAW kuma muka ci Gurasa da Nama tare da shi, ko kuma ya ce: Tharid, ya ce: sai na ce da shi: Manzon Allah SAW yayi Maka Istigfari? ya ce: Ey, haka ma kai sannan ya karanta wannan Ayar: "Kuma ka nemi gafarar zunubanka da kuma Muminai Maza da Mata" [Muhammad19: " ya ce: sannan na kewa bayansa sai naga Hatimin Annabta a tsakanin Kafaxunsa, a gefen Kafaxarsa na Hagu, kamar dunqulen hannu, akansa tabo, Kamar qwan tattabara, kuma ya sava da launin jikinsa SAW, kuma wannan baya savawa da riwayar da ta sifanta Hatimin da gashi ne da ya tattaru wuri xaya, da kuma wanda ya Kamanta ta Qwan Tattabara, to dukkan waxan can zai yiwu su taru wuri xaya.

Madogara

- صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي - بيروت. - المنهاج شرح صحيح مسلم بن الحجاج، للنووي، نشر: دار إحياء التراث العربي - بيروت، الطبعة: الثانية، 1392ه. - عمدة القاري شرح صحيح البخاري، لمحمود بن أحمد بن موسى الحنفى بدر الدين العينى، الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت. - معجم اللغة العربية المعاصرة، للدكتور أحمد مختار عبد الحميد عمر بمساعدة فريق عمل، الناشر: عالم الكتب، الطبعة: الأولى، 1429 هـ - 2008 م. - مرعاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح, أبو الحسن عبيد الله بن محمد الرحماني المباركفوري, الناشر: إدارة البحوث العلمية والدعوة والإفتاء، الجامعة السلفية، بنارس الهند, الطبعة: الثالثة - 1404 هـ، 1984 م - مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي بن سلطان الملا الهروي القاري، الناشر: دار الفكر، بيروت - لبنان، الطبعة: الأولى، 1422هـ - 2002م. - إكمال المعلم بفوائد مسلم لعياض بن موسى بن عياض بن عمرون اليحصبي السبتي، المحقق: الدكتور يحيى إسماعيل، الناشر: دار الوفاء للطباعة والنشر والتوزيع، مصر، الطبعة: الأولى، 1419 هـ - 1998 م. - الفتح الرباني لترتيب مسند الإمام أحمد بن حنبل الشيباني ومعه بلوغ الأماني من أسرار الفتح الرباني, أحمد بن عبد الرحمن بن محمد البنا الساعاتي, دار إحياء التراث العربي, الطبعة: الثانية.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
KEƁENCE-KEƁENCEN ANNABI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com