Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a cikin masallacinsa a tare da shi akwai sahabbansa, sai wani balaraben ƙauye ya zo daga ƙauye, sai ya zauna yana yin fitsari a grfen masallaci. Sai sahabbai suka yi masa tsawa suka ce: Tsaya tsaya. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ku ƙyale shi, kada ku yanke masa fitsarinsa, sai suka barshi har sai da ya gama. Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kirashi sai ya ce masa: Lallai masallatai badan fitsari aka yi su ba, ko nau'ikan ƙazanta ba, kawai su dan ambatan Allah ne - Mai girma da ɗaukaka -, da sallah, da kuma karatun alƙur'ani da makamancin haka. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya umarci wani mutum daga cikin sahabbai sai ya zo da guga cike da ruwa sai ya zuba akan fitsarinsa a hankali.
- Wajabcin girmama masallatai, da kuma tsaresu daga abinda ba ya kamata da su.
- Nawawi ya ce: A cikinsa akwai kiyaye masallatai da tsaftacesu daga ƙazanta da kaki, da ɗaga murya da rigima, da siye da siyarwa da sauran ƙulle-ƙullen abubuwa, da abinda ke da ma'anar haka.
- Sassautawa jahili da kuma sanar da shi abinda yake wajibinsa ba tare da tsanantawa ko cutarwa ba, idan bai zo da abinda ya saɓa ba, haka kawai dan wulaƙanci ko tsaurin kai.
- Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance malami ne mai tausayi, kuma mai ladabtarwa ne mai tausasawa, kuma mai tarbiyyantarwa ne mai juriya.
- Kwaɗaitarwa akan raya ɗakunan Allah - Maɗaukakin sarki - da yin sallah da kuma karatun alƙur'ani da kuma ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -.
صحيح البخاري (1/ 54) (221). صحيح مسلم (1/ 236) (285). نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1159). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (20/ 98). بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (3/ 191). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 436).