Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

‌Alƙiyama ba zata tashi ba har sai mutane sun dinga yin alfari da massalatai

عَنْ أَنَسٍ رَضيَ اللهُ عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لَا تَقُومُ السَّاعَةُ حَتَّى يَتَبَاهَى النَّاسُ فِي الْمَسَاجِدِ».
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «‌Alƙiyama ba zata tashi ba har sai mutane sun dinga yin alfari da massalatai».
Abu Dawud da Nasa'i da ibn Majah ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa: Yana daga cikin alamomin kusancin ranar alƙiyama da kuma ƙarewar duniya mutane zasu dinga alfahari da ƙawata masallatansu, ko kuma alfaharinsu da duniyarsu a cikin masallatan da ba'a ginasu ba sai dan ambatan Allah.

Fa’idoji
  1. Haramcin yin alfahari da masallatai, kuma hakan aiki ne ba karɓaɓɓe ba; domin ba'a aikata shi saboda Allah ba.
  2. Hani daga ƙawata masallatai da kaloli, da kuma fenti kala-kala da kuma zane-zane, da rubce-rubuce; dan abinda ke cikinsu na shagaltar da masallata a yayin kallonsu.
  3. Sindi ya ce: Wannan hadisin yana daga abinda duniya ta yi masa shaida, kuma hakan yana daga cikin jumlar mu'ujizoji bayyanannu gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Madogara

سنن أبي داود (1/ 337) (449). سنن النسائي (2/ 32) (689). سنن ابن ماجه (1/ 475) (739)،. توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، لعبد الله البسام (2/ 137). فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (1/ 621).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HUKUNCE-HUKUNCEN MASALLATAI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com