Cewa annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan yana sallah yana buɗa tsakanin hannayensa har sai farin hammatarsa ya bayyana
Daga Abdullahi ɗan Malik ɗan Buhainah - Allah Ya yarda da shi -: Cewa annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan yana sallah yana buɗa tsakanin hannayensa har sai farin hammatarsa ya bayyana.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi ya kasance idan zai yi sujjada yana buɗa tsakanin hannayensa a tsakiyar sujjada; sai kowanne hannu ya nisanta daga gefan da yake biye masa, kwatankwacin fukafukai biyu, har launin fatar hammatarsa ya bayyana; wannan yana daga kai matuƙa a nisantar da zira'i biyu da kuma nisantar da su daga sasanninsu.
Fa’idoji
An so wannan yanayin a cikin sujjada, shi ne nisantar da damatsansa biyu daga sasanninsa.
Mamun da na kusa da shi yake cutuwa da nisantarwar to ba'a shar’anta masa hakan ba.
Akwai hikimomi da fa'idoji masu yawa a cikin nisantar a cikin sujjada, daga cikinsu: Bayyanar da nishaɗi da kwaɗayi a cikin sallah, kuma idan ya dogara akan dukkan gaɓɓan sujjada sai kowacce gaɓa ta ɗauki haƙƙinta daga bauta. Akace: Hikima a cikin hakan ya yi kama da tawali'u, kuma mafi isuwa a cikin tabbatar da goshi da hanci a ƙasa, kuma dan banbance kowacce gaɓa da kanta.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 87) (390).
صحيح مسلم (1/ 356) (495).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص162).
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (2/ 207).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 134).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com